Sojoji sun ceto mata da yara 360 da aka sace a Gwoza

Army Army 700x430 (1)

Dakarun sojojin Najeriya na Operation Hadin Kai hadin gwiwar da Rundunar Ayyuka ta Musamman, sun ceto mutun 360, galibi mata da yara wadanda ‘yan ta’adda suka sace daga garin Ngoshe da ke Karamar Hukumar Gwoza ta Jihar Borno.

Manjo Janar Abdulsalam Abubakar, Kwamandan Operation Hadin Kai a Arewa maso Gabas, ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labaran na Kasa (NAN) cewa an samu nasarar ceton ne bayan wani aiki na musamman da aka gudanar na hadin-gwiwa a ranar 6 ga Yuni a wurare daban-daban da ke kewayen Dutsen Mandara.

Ya ce da fari Rundunar Ayyuka ta Musamman ta fara gudanar da wasu ayyuka da suka jefa sansanonin ‘yan ta’adda cikin rudanin, lamarin da ya baiwa sojojin Rundunar ta 26 Task Force damar ceto wadanda aka rike da su cikin nasara.

“mutanen da aka ceto suna daga cikin mazauna garin Ngoshe da ‘yan ta’adda suka sace yayin harin da suka kai a ranar 3 ga Maris 2026.

“Sai dai kuma, a yayin aikin wani abun takaici yara jarirai 2 sun mutu yayin da ake kokarin ceto saboda wuya da muni yanayin tafiya da wadanda abin ya shafa zuwa wuri mai tsaro,” in ji shi.

Ya kara da cewa an yi wa duk wadanda aka ceto gwajin lafiya nan da nan da suka isa, yayin da wadanda ke bukatar kulawar lafiya ta gaggawa sojojin Rundunar na kula da lafiya suka daidaita lafiyarsu aka kwantar da su a Babban Asibitin na Gwoza domin jinya.

“An kuma basu abinci da ruwa kafin a kai su wani wuri da za a zaunar da su na tsaro yayin da ake jira a mika su ga hukumomin da suka dace domin sake hada su da iyalan su,” in ji shi. NAN

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here