Na gaji Naira miliyan 4 kacal, tare da tarin basuka daga Matawalle – Gwamna Lawal

L R Bello Matawalle and Dauda Lawal

Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya bayyana irin kalubalen da gwamnatin sa ta fuskanta tun bayan hawansa mulki.

A wata hira da ya yi da tashar talabijin ta Arise a ranar Litinin, Lawal ya bayyana cewa lokacin da ya karbi mulki daga hannun tsohon gwamna Bello Matawalle, jihar Zamfara ta kasance cikin “rikici ta kowane fanni” da rashin tsaro da tabarbarewar tsarin ilimi, lafiya da basussuka.

“Lokacin da na hau mulki jihar Zamfara ta kasance cikin rudani a kowane fanni na rayuwa, walau tsaro a mataki mafi girma, ilimi a kasa, kiwon lafiya a kasa, karfin ci gaban bil’adama kusan babu shi, kuma dalili daya ne ya sa na sanya dokar ta-baci a fannin ilimi da kiwon lafiya.

Karin karatu: Masu neman aiki su 8 sun fadi a gwajin ƙwaya da TESCOM ta yi musu

“Ba digon ruwa ko digo daya na tsawon watanni biyar a Jihar Zamfara lokacin da na karbi ragamar mulki, kuma a cikin kwanaki uku kacal muka samu nasarar shawo kan lamarin, don haka a gaskiya abin da ake bin bashin ya kasance abin da ba za a iya mantawa da shi ba, amma a matsayina na jagora, sai da na nemo hanyar da zan iya daukar nauyin hakan,” inji shi.

Lawal ya kuma bayyana yadda gwamnatin sa ta yi wa fannin ilimi garambawul, wanda ke cikin mawuyacin hali da kuma magance matsalolin kudi a fannin.

Da yake magana kan tsaro, Lawal ya bayyana cewa gwamnatinsa na kokarin rage tashe-tashen hankula.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here