Gwamnatin Zamfara ta fayyace dalilan rufe wasu kasuwannin dabbobi a jihar

Zamfara, Dauda Lawal, man fetu, burodi
Zamfara Gov. Dauda Lawal

Gwamnatin jihar Zamfara ta bayyana dalilin rufe wasu kasuwannin dabbobi a jihar.

A ranar Laraba ne gwamnatin jihar ta sanar da rufe kasuwannin a kananan hukumomi bakwai wadanda ta ce ana hada-hadar shanu da dabbobin sata.

Kwamishinan yada labarai na jihar Mannir Haidara Kaura, shi ne ya bayyana hakan da yammacin laraba.

Yace dauki wannan mataki ne a wani yunkuri na tabbatar da kare rayuka da dukiyoyin jama’ar jihar.

Karanta wannan: Shettima ya kaddamar da sabon Ofishin Gwamnan Kano da aka sake wa fasali

Ya ce bayanan da gwamnati da hukumomin tsaro suka samu sun nuna cewa yan fashin daji na shigo da dabbobin da suka kwace a hannun mutane.

Acewarsa yan fashin kuma suna cinikin dabbobin inda suke samun kudin da suke gudanar da harkokinsu na yau da kullum.

Ba dai wannan ne karon farko da gwamnatin jihar ta Zamfara ke rufe kasuwannin dabbobi ba, bisa zargin hada-hadar dabbobin sata da yan fashin daji ke yi.

A watan Satumba ma akwai wasu kasuwanni guda bakwai da gwamnatin jihar ta rufe saboda irin wannan zargi, inda ake ci gaba da bincike.

Jihar Zamfara dai na daya daga cikin jihohin da suka fi fama da matsalar tsaro a Najeriya, inda yan fashin daji ke kai hare-hare, suna kashe jama’a.

Sai dai gwamnatin jihar na ganin cewa irin wadannan matakai da take dauka, za su taimaka wajen shawo kan matsalar da ta ki ci ta ki cinyewa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here