Kashe-kashen Filato: ‘Yan majalisar wakilan Arewa sun nemi a gudanar da bincike

Alhassan Ado Doguwa.jpeg
Alhassan Ado Doguwa.jpeg

Kungiyar ‘yan majalisar Wakilan Arewa ta yi Allah wadai da kisan gillar da aka yi wa sama da mutane 155 a jihar Filato.

Shugaban kungiyar Alhassan Ado Doguwa wanda ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a Abuja ranar Alhamis, ya bukaci a gudanar da cikakken bincike a kan lamarin.

Karanta wannan: Gwamnatin Zamfara ta fayyace dalilan rufe wasu kasuwannin dabbobi a jihar

Ya ci gaba da cewa, “Kungiyar ‘yan majalisar wakilai ta Arewa ta samu labarin kisan gillar da aka yi wa mutane a kauyuka 23 da ke kananan hukumomin Bokkos da Barikin Ladi na jihar Filato.

“Da farko, muna son mu jajanta wa gwamnati da mutanen jihar Filato, sannan mu yi tir da wannan kashe-kashen na zalunci da rashin hankali.

“Wadannan ayyukan ta’addanci bai kamata a zuba ido ana gani su ci gaba da faruwa ba. Yankin arewa an san mu da zaman lafiya.

“Daga rahoton da kafafen yada labarai suka fitar ya nuna adadin wadanda suka rasa rayukansu a hare-haren ya kai sama da 150, saboda haka dole mu nuna bacin ran mu’’.

Kuma mun hada kai yanzu muna neman a yi cikakken bincike kan lamarin, domin yana jefa yankin mu cikin mummunan yanayi na kasa baki daya.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here