Shugaban karamar hukuma ya mutu a jihar Kebbi

kebbi lg chairman muhammad bello is dead
kebbi lg chairman muhammad bello is dead

Shugaban karamar hukumar Maiyama ta jihar Kebbi Honorable Zayyanu Muhammad Bello, ya rasu.

Mai Magana da yawun gwamnan jihar Kebbi Ahmed Idris, ne ya tabbatar da mutuwar sa a wata sanarwa ya fitar ranar Alhamis.

A statement issued by the Spokesperson for Kebbi State Governor, Ahmed Idris, on Thursday, confirmed the development.

Sanarwar tace Bello, ya rasu ne bayan fama da doguwar Jinya.

Karanta wannan: Kashe-kashen Filato: ‘Yan majalisar wakilan Arewa sun nemi a gudanar da bincike

A cewar sanarwar shuagaban karamar hukumar ya rasu ne da safiyar Alhamis din nan a Asibitin koyarwa na jami’ar Usman Danfodio dake Sokoto.

Ta kara da cewa nan gaba gwamnatin jihar zata sanar da wuri da kuma lokacin da za’a yi jana’izar sa kamar yadda addini ya tsara.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here