An kuɓutar da mata 66 da aka sace a Burkina Faso

FB IMG 16742981541935961
FB IMG 16742981541935961

Kafar yaɗa labarai ta gwamnatin Burkina Faso ta ce wasu taron mata 66 da yara, waɗanda masu iƙirarin jihadi suka sace a arewacin ƙasar a makon da ya wuce, sun samu kansu.

Tashar rediyon ƙasar ta ce jami’an tsaro ne suka ceto su.

An sace mutanen ne wadanda suke kalen abinci a daji a yankin da ya kasance kewaye da masu ikirarin jihadi.

Wannan dai ita ce satar mutane masu yawa da ta fito fili a Burkina Faso, ƙasar da rikicin ƙungiyoyin wadannan mayaƙa da sauran rigingimu suka tilasta wa mutane sama da miliyan biyu tserewa daga muhallansu.

An yi kwanaki da dama kafin gwamnatin mulkin soja ta ƙasar ta yadda cewa an sace matan da yara.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here