Ƙungiyar ƙwararrun likitoci ta ƙasa ta sanar da cewa za ta fara yajin aiki na ƙasa gaba ɗaya daga ranar 1 ga watan Nuwamba.
Wannan matakin ya biyo bayan taron majalisar zartarwa ta ƙasa ta ƙungiyar wanda aka ɗauki sa’o’i biyar ana yin sa a ranar Asabar.
A cewar shugaban ƙungiyar, Dakta Mohammad Suleiman, sanarwar yajin aikin ta fito ne bayan karewar wa’adin kwanaki 30 da ƙungiyar ta bai wa gwamnatin tarayya kan wasu buƙatu da ba a warware ba.
Ƙungiyar ta ce, ta gaji da jinkirin da gwamnati ke yi wajen aiwatar da yarjejeniyar da aka cimma a baya tare da magance matsalolin alawus da yanayin aiki.
Ta ƙara da cewa za ta ci gaba da yajin aikin har sai gwamnati ta amsa cikakkun buƙatunta.













































