Ƙungiyar Ma’aikatan Man Fetur da iskar Gas (NUPENG) ta sanar da cewa za ta fara yajin aiki na ƙasa baki ɗaya daga Litinin, 8 ga Satumba, 2025, saboda abin da ta kira cin zarafin ƙungiyoyin kwadago da ke tattare da shigo da sabbin motocin iskar gas (CNG) daga Kamfanin Man Dangote.
A wata sanarwa da Shugaban ƙungiyar na Ƙasa Prince Williams Akporeha, tare da Sakataren Ƙasa, Afolabi Olawale, suka sanya wa hannu, NUPENG ta bayyana cewa Dangote ya fara shigo da motocin CNG har 10,000 don rarraba man fetur da dizal, amma tsarin amfani da su na kawar da ƙungiyoyin kwadago da ake da su a fannin.
Ƙungiyar ta zargi kamfanin da fara ɗaukar direbobin motocin a ranar 29 ga Agusta, inda ake tilasta masu neman aikin su rattaba hannu kan yarjejeniya da ta haramta shiga ƙungiyoyin kwadago, abin da ta ce ya saba wa Kundin tsarin mulkin Najeriya, dokar ƙungiyar ƙwadago da yarjejeniyoyin ƙasa da ƙasa ta ILO.
Karanta: Hukumar NAHCON ta sanar da sauye-sauye a ma’aikatanta
NUPENG ta jaddada cewa sashe na 40 na Kundin Tsarin Mulki da sashe na 9(6) na dokar Kwadago suna ba da dama ga ma’aikata su shiga ko kada su shiga ƙungiya, haka kuma Najeriya ta amince da yarjejeniyar ILO mai lamba 87 wacce ta tanadi ‘yancin haɗin gwiwa.
Ƙungiyar ta kuma nemi Hukumar NMDPRA ta yi amfani da ikon da ta yi ke da shi a ƙarƙashin dokar PIA domin hana cin moriyar da zai tauye gasa a bangaren rarraba mai.
Bayan cece-kuce da ƙoƙarin tattaunawa da hukumomi ba tare da samun mafita ba, NUPENG ta ce ba ta da wani zaɓi illa shiga yajin aiki, tana mai roƙon ‘yan Najeriya da su fahimci cewa matakin na kare haƙƙin ma’aikata ne, tare da neman haɗin kai daga NLC da TUC.













































