Majalisar zartarwa ta tarayya ta amince da kwangilar da ta kai Naira biliyan 6 domin gudanar da aikin samar da ruwan noman rani na Chochi a jihar Adamawa da kuma naira biliyan 1 da milyan dari 4 don siyan kayan aikin jiragen sama.
Ministocin albarkatun ruwa, Sulieman Adamu, da sufurin jiragen sama, Hadi Sirika, ne suka bayyana haka a lokacin da suke zantawa da manema labarai a fadar shugaban kasa bayan kammala taron majalisar zartarwar da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranta a ranar Laraba.
Adamu ya ce: “Kamar yadda kuka sani burinmu tun farkon wannan gwamnati shi ne kammala ayyukan da muka gada.
A cewarsa, sakamakon karin Naira biliyan 6 da aka yi yanzu aikin ya Kai Naira biliyan 11 da miliyan 26 tare da karin wa’adin watanni 24, da kuma tsawon watanni 12, wanda ya kai watanni 36.
A nasa bangaren, Sirika ya ce an amince da Naira biliyan 1 da miliyan dari 4 ne don siyan kayan aikin kula da filayen jiragen sama na Kaduna da Fatakwal.
Ya ce: “Amincewar ta biyo bayan bayar da kwangilar tsarawa da samarwa tare da kula da na’urorin lura da wadannan filayen jiragen sama na Fatakwal da Kaduna ne kuma za a ci gaba da zuwa sauran filayen jiragen sama a hankali.
Sirika ya kuma sanar da cewa majalisar ta amince da yarjejeniyar zirga-zirgar jiragen sama tsakanin Najeriya da Canada.