Hukumar kula da sufurin Jiragen sama ta Kasa (NCAA) ta dakatar da lasisin kamfanin zirga-zirgar jiragen sama na Dana Airlines (ATL) da shaidarsa ta gudanar da aiki har sai abinda hali ya yi, Kuma zata fara aiki be daga tsakar daren Laraba, 20 ga watan Yulin 2022.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun Darakta Janar na hukumar Kyaftin Musa Nuhu, ranar Laraba a Legas.
Sanarwar ta ce an dakatar da kamfanin ne dogaro ga sashe na 35 (2 cikin baka) da karamin sashe na 3 (b cikin baka) da (4 cikin baka) na dokar zirga-zirgar jiragen sama na shekarar 2006 da kuma sashi na 1.3.3.3 (a) (1) na dokokin zirga-zirgar jiragen sama na Najeriya (Nig. CARs), 2015.
A cewar sanarwar, an yanke hukuncin ne sakamakon wani binciken kudi da tattalin arziki da hukumar ta gudanar a kan kamfanin, da kuma sakamakon binciken da aka gudanar kan ayyukan jirgin na kamfanin a baya bayan nan.
Kamfanin dillancin labarai na Kasa (NAN) ya rawaito cewa jirgin Dana Air Boeing 737 mai lamba (5N DNA) ya yi saukar gaggawa a filin jirgin saman Abuja a ranar Talata.

Kamfanin jirgin, bayan faruwar lamarin, ya ce an dakatar da jirgin domin samun kulawa cikin gaggawa daga injiniyoyi.
Manajan sashen yada labaran Kamfanin, Mista Kingsley Ezenwa, shi be ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar a Legas.
Ezenwa, ya ce lamarin ya faru ne sakamakon wata alama da aka samu a daya daga cikin injinan ta.
Ya yi nuni da cewa, matukin jirgin ya yi wa fasinjoji bayanin lamarin, sannan ya sauka da jirgin lafiya a filin jirgin saman Abuja da misalin karfe 2 da mintuna 52 na rana.
Ezenwa ya nemi afuwar fasinjojin da ke cikin jirgin tare da tabbatar wa abokan huldar kamfanin cewa kamfanin zai ci gaba da kiyaye ka’idojin tsaro.
Har ila yau, dakatar da aikin DANA Air na zuwa ne jim kadan bayan da Ma’aikatan Jiragen Saman na Najeriya suka rubutawa Hukumar NCAA da Hukumar Kula da filayen Jiragen Sama ta Kasa wasika inda suka bayyana wasu matsaloli tare da neman agaji.













































