Jami’an EFCC suna gudanar da bincike a babban ofishin Dangote hada-hadar kudaden kasashen waje

EFCC Operatives 1
EFCC Operatives 1

Jami’an hukumar yaki da cin hanci da rashawa EFCC ta na ci gaba da gudanar da bincike a babban ofishin kamkanin Dangote dake Legas.

EFCC na gudanar da bincike ne kan harkallar kudaden da ake ware wa kamfanin tun lokacin Godwin Emefiele na matsayin gwamnan babban bankin kasa.

Karanta wannan: Mutum 2 sun mutu a hatsarin da tawagar Mataimakin Gwamnan Sokoto ta yi

Mai Magana da yawun hukumar ta EFCC Dele Oyewale, ne ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya fitar.

Karanta wannan: Tsohuwar ministar jin ƙai ta yi martani kan zargin ta da ake da almundahanar naira biliyan 37

Wata majiya daga babban ofishin na Dangote ta ce jami’an na neman takardu kan hada-hadar kudaden kasashen waje da kuma bankin na CBN.

Muna tafe da Karin bayani………

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here