Yan sandan Najeriya ta kama wani mutumi ɗan shekara 32 a duniya mai suna, Yusuf Isah, bisa zargin yana da hannu a harin da aka kai wa babban Malamin coci.
Mutumin ya shiga hannu ne kan zargin alaƙa da kazamin harin da aka kai wa babban Fasto kuma shugaban mabiya Omega Fire Ministries na duniya, Johnson Suleman.
Idan baku manta ba a watan Oktoba, 2022, wasu miyagun ‘yan bindiga suka farmaki ayarin motocin fitaccen Faston a kan titin Benin-Auchi cikin jihar Edo.
Yayin wannan hari, ‘yan bindigan sun halaka mutane shida kuma daga cikinsu harda jami’an hukumar ‘yan sanda guda uku.
Ya ce yan sanda sun kwato bindigun AK-47 guda 5, bindigun K2 guda biyu da alburusai 180 daga hannun wanda ake zargi.
“Bayan bincike mai zurfi dangane da harin da aka kai wa ayarin Fasto, Apostle Johnson Suleman, jami’an sashin FIB-IRT sun kama Yusuf Isah ɗan asalin garin Okene, jihar Kogi kuma yana sana’a a Akure, jihar Ondo.” “An samun bindigun Ak47 guda biyar, bindiga ƙirar K2 guda biyu, alburusai guda 180 da kuma wasu abubuwan fashewa 4 a gidan da yake zama.”