Rashin tsaro: Tinubu ya gana da Ribadu da babban hafsan tsaro

Tinubu Bola 750x430

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya kira wani babban taron tsaro a ranar Laraba tare da mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro Nuhu Ribadu da babban hafsan tsaron kasa (CDS) Janar Christopher Musa a fadar sa dake Abuja.

Taron dai na zuwa ne a daidai lokacin da ake samun tashe-tashen hankula a sassan kasar nan, musamman a jihohin Filato da Binuwai.

Shugaba Tinubu, wanda ya dawo daga ziyarar aiki ta kwanaki 19 daga Turai a yammacin ranar Litinin, ana sa ran zai samu bayanai daga manyan jami’an tsaro da na leken asirinsa kan halin da ake ciki a yankunan da suka fuskanci tashe-tashen hankula da zubar da jini a ‘yan kwanakin nan.

Matsalar tsaro ta kara tabarbarewa a jihohin Filato da Binuwai, inda rahotanni ke cewa wasu da ake zargin makiyaya ne daga kasashen waje suka kai ga asarar rayuka da kuma raba mazauna yankin da muhallansu.

Karanta: Yanzu-yanzu: Tsohon gwamnan jihar Delta Okowa ya fice daga PDP, ya koma APC

Rikicin da ke ci gaba da haifar da damuwa a cikin gida da waje, tare da yin kira da a dauki kwararan matakai don dawo da zaman lafiya da tsaro a yankunan da lamarin ya shafa.

Ana ganin ganawar ta Shugaba Tinubu da NSA da CDS a matsayin wani muhimmin mataki na magance matsalolin tsaro da kuma ba da agaji ga al’ummomin da suka tagayyara.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here