Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf ya raba filaye 1,540 tare da tallafin kudi naira miliyan 100 ga shugabannin Kungiyar ‘Yan Akwati na jam’iyyar APC, a matsayin wani mataki na tabbatar da kokarin karfafa tsarin jam’iyyar a mataki na kasa gabanin babban zaben shekarar 2027.
Wannan bayani na kunshe a cikin wata sanarwa da kakakin Gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar ranar Laraba.
Gwamnan ya sanar da wannan tallafi ne lokacin da yake kaddamar da kungiyar ta ’Yan Akwati a hukumance, inda ya bayyana tsarin akwati a matsayin kashin bayan karfin zaben jam’iyyar APC.
Gwamna Yusuf ya bayyana cewa karfafa magoya bayan na kasa zai bunkasa kokarin taron gangamin jam’iyyar tare da tabbatar da nasarar tazarce ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ma sauran ‘yan takarar APC a zabuka masu zuwa.
Ya nuna cewa sake zabar Shugaba Tinubu zai tabbatar da dorewar sauye-sauyen tattalin arziki da ayyukan cigaban da ke gudana a fadin kasar nan.
A cewar gwamnan, kyautar filayen da kuma tallafin naira miliyan 100 na da nufin kwadaitar da membobin kungiyar domin su gudanar da ayyukan jam’iyya yadda ya kamata a matakin akwatin zabe.
Tun farko, Babban Mai Taimakawa Gwamna na Musamman kan Al’amuran Siyasa, Mustapha Hamza Buhari Bakwana, ya bayyana wannan tallafi a matsayin mataki na farko na babban shirin hada karfi da karfe a jam’iyyar APC a matakin kasa gabanin zaben 2027.
Ya bayyana kwarin gwiwar cewa hanyar sadarwa ta ’Yan Akwati tana da karfin tara kuri’u sama da miliyan daya ga Shugaba Tinubu a Jihar Kano.
Taron ya sami halartar shugabannin jam’iyya, masu ruwa da tsaki a harkar siyasa da kuma wakilan kungiyar da aka zabo daga dukkan Karamar Hukumomi 44 na jihar.












































