-Na Jamilu Abdussalam Hajaj
Kanawa ku zo mu dan zanta garin Dabo ba na Babawa ba,
Batu gare ni ba babatu ba,
Zancen ilmin matasa ba na siyasa ba,
Ba kuma kin auratayyar matasan na ke kyamata ba,
Sai dai nuni ga gwamna, aikin kamar akwai ganganci.
Ba zambo zani yi ga shugabanci ba,
Ba kuma kushe na ke nufi ga aikin Gwamna ba,
Ba hassada ba ce ga masu auren riba ba,
Sai dai nuni ga Gwamna, aikin kamar akwai ganganci.
Suna na Jamilu Dan Abdussalamu,
Da sunan Rabbi Allah mahallincin Dan Adamu,
Wanda ya umarci yin ilimi har ya kasance wajibi a kan mu,
Ya kuma ce mu yi aure idan har muna da damar mu,
Domin ciyarwa da shayarwa da tufar kullum duk sun rataya kan wuyoyin mu,
Sai na ga wani abu bahui kamar ba a kano ba,
A ce kudin auratayya ya daram ma na ilimin jagororin mu nan gaba?
Sai na ga kamar koma-bayan mu kan ilimi ya fi karfin wani batu ya fi shi kan gaba,
Talauci da ilimi fa su su ka hana kasancewa mu a can gaba,
Ni dai nuni na ke ga Gwamna, aikin kamar akwai ganganci.
Jama’a tambaya gareni a kan wajibjin aure,
To ko da nauyin hidimar aure, mazan sakinki su ke kamar ba gobe,
Ya yi lefe, sadaki da da duk shagalin aure,
Balle a ce gwamnati dare guda ta so ta ba ka ka more,
Kai ka san kuwa sai dai Ilahi ya sa alakar auren da dore,
A ce ba ka ga tsuntsun ba ga tarko?
Gwamna, wannan aikin dai kamar akwai gangaci.