Boko Haram ta mamaye makaranta, ana fargabar an sace dalibai da dama a Borno

Boko Haram (1)

Ana fargabar an sace dalibai da ba a tantance adadinsu ba na Makarantar Firamare da Sakandaren Mussa da ke Karamar Hukumar Askira-Uba a Jihar Borno, lokacin da wasu ‘yan ta’addan Boko Haram/ISWAP masu dauke da makamai suka mamaye harabar makarantar da sanyin safiyar Juma’a.

Mussa kauye ne mai nisa kuma yana da iyaka da Dajin Sambisa, wani wurin buyae da ‘yan ta’adda ke amfani da shi.

Majiyoyi sun bayyana cewa ‘yan ta’addan sun shiga makarantar ne da babura, kusan mintuna 10 zuwa 15 bayan sojoji sun fice daga yankin.

A wani sako da ya wallafa a shafin sada zumunta, Mista Solomon Mussa ya ce, “Barka da safiya, masoya. Ku yi addu’a a kan harin Boko Haram da ya auku a kauyen Mussa yanzu, dangane da rahoton da ke fitowa daga Mussa, ya kuma shafi daliban makaranta…”

A halin yanzu, Mataimakin Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Borno, Rt Hon. Abdullahi Askira, wanda shi ma dan asalin Karamar Hukumar Askira-Uba ne, ya tabbatar da mamayar da ‘yan ta’addan suka yi wa makarantar a ranar Juma’a, kodayake ya ce bayanan har yanzu ba su cika ba a lokacin da ake rubuta labarin.

“Eh, zan iya tabbatar muku cewa wasu ‘yan ta’adda da ake zargi da ke kan babura sun mamaye makarantun firamare da sakandare a kauyen Mussa da safiyar yau.

Bayanan da ke hannuna sun nuna cewa yawancin daliban sun gudu zuwa daji, amma ba ni da cikakken bayani kan wadanda aka sace tukuna.

Haka kuma abin takaici ne cewa lamarin ya faru ne kusan ‘yan mintuna kadan bayan sojojin da ke sintiri sun fice daga yankin, wannan yana nuna cewa ‘yan ta’adda ko maharan sun kasance suna sa ido kan motsin sojoji kafin su kai hari,” in ji Mataimakin Kakakin.

Duk da haka, ya yi alkawarin bayar da karin bayani yayin da lamarin ke kara bayyana.

Hukumomin ‘yan sanda ba su ce komai ba tukuna kan lamarin.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here