Idan dai ba’a manta ba a ranar Litinin da ta gabata ne Jarumar Shirya Fina-finan Hausa ta Kannywood, Fatima Hussaini da aka fi sani da Maryam ta cikin fim mai dogon zango na Labarina ta samu kyautar dankareriyar mota ta kimanin Naira Miliyan 6 daga wani bawan Allah.
Wata majiya ta bayyana mana cewa mutumin ya kasance mai kallon shirin fim din Labarina ne akoda yaushe, kuma masoyin Maryam ta cikin shirin, hakan ce ta bashi damar yiwa jaruma Fatima kyautar Mota.
Karanta wannan: Gobara ta Lalata kasuwar Panteka dake Kaduna
Mutumin ya ce “Ya mata kyautar motar ne, Sakamakon yadda ta nuna gudun dukiya a cikin shirin Labarina, hakan ya burgeshi sosai.”
To sai dai tun bayan samun kyautar motar ne al’umma da dama suka cigaba da cecekuce tare da bayyana ra’ayoyinsu kan wannan al’amari, inda wasu ke ganin kyautar ba tsakani da Allah akayi ta ba, wata manufa ce kawai ta daban.
Wasu na ganin akwai jarumai dadaddu maza da mata da suka shahara suke bukatar taimako, a masana’antar.
Sannan akwai marubuta da masu shiryawa da masu bada umarni da kuma masu daukar hoto wadanda ake kallon sune jigon samar da ayyukan jaruman masana’antar.
Karanta wannan: Gwamnatin Kano za ta kashewa makarantun firamare 3 Naira Biliyan 8
Kazalika, wasu na ganin akwai mabukata da marayu da marasa lafiya da ke bukatar neman taimako. Amma ba’a bi tsarin da ya kamata ba, kasancewar ana ganin kamar Fatima tayi shigar wuri a masana’antar shirya fina-finan Hausa.
Wasu kuma na ganin cewar, “Hakan yayi daidai suna goyon bayan yin wannan kyauta, watakila ma hanyar samun mijin auren ta ne yazo” A cewar wasu.
Saidai akwai fina-finai da dama da jarumar ta dade tana taka rawa a masana’antar tauraruwar ta bata bayyana ba sai a fina-finai na (Na Ladidi da Labarina).
Tuni dai al’umma ke cigaba da wallafa ra’ayoyin su kan wannan lamari a dandalin shafukan sada zumunta daban-daban.