Al’ummar Gabon sun fito kan tituna domin nuna goyon bayansu ga juyin mulkin da sojoji suka yi wa shugabansu Ali Bongo.
Juyin mulkin ya afku ne da sanyin safiyar yau Laraba bayan da aka ayyana Ali Bongo a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa karo na uku.
Da aka bayyana sakamakon zaben, jami’an soji sun umurci gidan talabijin na kasar da su ayyana zaben haramtatce tare da karbar ragamar mulki a madadin shugaban kasar da ya kwashe shekaru 14 yana gwamnati.
Ali Bongo ya gaji mahaifinsa, wanda ya shafe shekaru 42 yana mulki. A jimilce shekaru 56, dangin Bongo ke mulki.













































