Majalisar dokokin ta jihar Kano, ta tabbatar da karbar wata wasika daga gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf, inda yake neman majalisar da ta tantance mutumin da yake son nadawa a matsayin mataikakin gwamna, Hon Murtala Sule Garo.
Kakakin majalisar dokoki ta jihar Kano, Hon Ismail Jibrin Falgore ne ya sanar da hakan, bayan karanta wasikar da gwamnan ya aike wa majalisar a ranar Laraba.
Jaridar SolaceBase ta rawaito Gwamna Abba Kabir Yusuf na neman nada Murtala Sule Garo ne a matsayi mataimakin gwamna bayan da tsohon mataimakin gwamnan Comrade Aminu Abdussalam Gwarzo ya ajiye aiki a watan da ya gabata.
A cikin wasikar, gwamnan ya bayyana Garo a matsayin mutum mai kyawawan dabi’u da gogewa da kuma ci gaban da ya baiwa jam’iyyar APC da jihar Kano a mukaman da ya rike a baya.
Bukatar nadin, dama ce da sashi na 191(3) na kundun tsarin mulkin kasa 1999 da aka yiwa kwaskwarima ya baiwa gwamnan ya zabi mataimakin na shi domin cike gurbi.
Bayan karanta wasikar, kakakin majalisar dokokin ya sanar da kafa kwamitin wucin gadi da zai tantance Garon.
Kwamitin da mataimakin kakakin majalisar zai jagoranta ya hada da, shugaban masu rinjayi na majalisar da bulaliyar majalisa da mataimakin shugaban masu rinjayi. Sauran sun hada da danmajalisa Fagge da na Sumaila da Warawa da Dawakin kudu sai kuma na Tudun Wada da sauransu.
Ana sa ran kwamitin zai gayyaci Garo don tantancewa tare da gabatar da jawabi ga majalisar a ranar Litinin.
A cewar sanarwar, Murtala Sule Garo mai shekarar 48 gogaggen dansiyasa ne da ya shafe sama da shekara ashirin yana siyasa a matakai da dama na zababbe da kuma nadi.
Cikin mukaman da ya rike, Murtala ya taba zama sakataren shirye-shiryen jam’iyya, ya kuma taba zama mashawarci na musamman ga gwamna Kano kafin daga bisani a zabe shi a matsayin shugaban karamar hukumar Kabo.
Ya kuma taba zama shugaban shugabannin kananan hukumomi na jihar Kano, kwamishinan kananan hukumomi da masarautu na jihar, yayin da a zaben 2023 ya yi takarar mataimakin gwamna a jam’iyyar APC.












































