Hukumar Zabe ta bayyana manyan kalubale shida dake barazana ga zaben 2027

Joash Amupitan INEC (1)

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta bayyana manyan kalubale guda shida da ke barazana ga babban zaben shekarar 2027.

Shugaban hukumar, Prof. Joash Amupitan SAN, ne ya bayyana hakan a ranar Talata a birnin Abuja, yayin da yake karbar bakuncin tawagar tantance shirin zabe (PEAM) ta cibiyar International Republican Institute (IRI), karkashin jagorancin tsohuwar mataimakiyar sakataren harkokin wajen Amurka kan al’amuran Afirka, Ambasada Jendayi Frazier.

Amupitan ya bayyana cewa wadannan barazanoni na iya taba kwarin gwiwar masu kada kuri’a tare da haifar da gagarumin kalubale ga tsarin zaben idan ba a shawo kansu cikin gaggawa ba.

Manyan barazana guda shida da hukumar ta gano sun hada da:
Barazanar tsaro
Rikicin zabe a wasu takamaiman yankuna
Sayen kuri’a
Kalaman kiyayya
Yada labaran karya (Disinformation)
Katsalandan din kasashen waje cikin tsarin zabe (FIMI)

Wannan ziyara ta zo ne kwanaki uku bayan gudanar da zaben gwamna na jihar Osun, kuma kwana guda kafin fara kamfen din zaben 2027 a hukumance ranar Laraba, 19 ga watan Agusta.

Shugaban na INEC ya kara da cewa wannan tawagar tantancewa ta samar da kyakkyawan hangen nesa mai zaman kansa yayin da hukumar ke tsunduma cikin shirin gadan-gadan domin zaben 2027.
Ya bayyana cewa INEC na kara fadada nagartar aikinta don tura ma’aikatan wucin gadi kusan miliyan 1.4 zuwa rumfunan zabe sama da 176,000 a fadin kasar yayin zabukan na 2027.

Haka zalika, Amupitan ya bayyana cewa hukumar na amfani da tsarin tantance shaidar ‘yan kasa na Automated Biometric Identification System (ABIS), karkashin tsarin rajistar masu zabe ta dindindin (CVR), don ganowa tare da goge sunayen mutanen da suka yi rajista sau biyu domin samun tsaftatacciyar Rajistar Masu Zabe ta Kasa.

A cewarsa, zabukan gwamna na baya-bayan nan da zabukan cike gurbi na majalisu sun zama gwajin aiki ga tsarin adana kayan aiki, daidaiton tsaro da kuma tsarin fasahar hukumar.

Ya bayyana cewa amfani da fasaha ya rage matsalolin da ke tattare da tsarin jefa kuri’a na baya a Najeriya.

“Sakamakon aikin na’urar tantance masu zabe ta (BVAS) da kuma nuna sakamakon rumfunan zabe kai tsaye a dandalin bibiyar sakamakon zabe (IReV) na ci gaba da nuna inganci mai kyau, inda aka samu nasarar daura sakamako sama da kashi 98 cikin dari a zabukan gwaji na baya-bayan nan,” in ji shi.

Amupitan ya ce tsarin aikin hukumar ya hada da binciken rajistar masu zabe, shirye-shiryen tura kayan aiki da wuri tare da hadin gwiwar kungiyoyin sufuri don tabbatar da an bude rumfunan zabe da karfe 8:30 na safe da kuma inganta kayan bada tallafi ga masu bukata ta musamman, mata masu juna biyu da tsofaffi.

Game da barazanar tsaro da na kudi, ya ce INEC na aiki tare da hukumomin tsaro karkashin Kwamitin Shawara na Tsakanin hukumomi kan Tsaron Zabe (ICCES), da kuma hukumomin yaki da rashawa EFCC da ICPC.

Ya ce wannan hadin gwiwa na nufin sanya ido kan kudaden yakin neman zabe, lura da laifukan zabe da kuma tabbatar da cewa an hukunta wadanda suka taka doka.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here