Tinubu zai tafi Guinea-Bissau taron ECOWAS

Tinubu Returns 2
Tinubu Returns 2

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu zai halarci taron shugabannin ƙasashen ƙungiyar ECOWAS karo na 63 da za a gudanar a ƙasar Guinea-Bissau.

A wata sanarwa da mai bai wa shugaban ƙasar shawara kan ayyukan na musamman Dele Alake ya fitar, ya ce shugaban zai bar Najeriya a yau Asabar domin halartar taron wanda za a gudanar ranar Lahadi.

Sanarwar ta ce shugaban zai samu rakiyar wasu daga cikin masu ba shi shawara tare da wasu manyan jami’an gwamnatinsa.

Ana sa ran tattauna muhimman batutuwan da ke damun ƙasashen ƙungiyar ciki har da matsalar tsaro da ƙasashen yankin ke fuskanta, tare da yin nazari kan rahoton da majalisar ministocin ƙungiyar suka fitar a taronsu na 90 da suka gudanar.

Haka kuma akwai batun hulɗar kasuwanci tsakanin ƙasashen Afirka tare da yin nazari kan batun miƙa mulki hannun farar hula a ƙasashen Mali da Burkina Faso da kuma Guinea.

Sauran batutuwan da ake sa ran taron zai tattauna sun haɗar da batun kudin bai ɗaya na ƙungiyar, da matsalar da ake samu wajen safarar kayayyaki tsakanin wasu ƙasashen yankin.

Wannan shi ne karo na biyu da shugaban ƙasar zai halarci taro a ƙasashen waje tun bayan rantsar da shi a matsayin shugaban ƙasar ranar 29 ga watan Mayu.

Taro na farko da Tinubu ya halarta a ƙasashen waje, shi ne taron harkokin kuɗi da ya gudana a Faransa cikin watan Yuni.

Ana ra ran shugaban ƙasar zai koma Najeriya bayan kammala taron

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here