Gwamnatin Kano ta kaddamar da ayyukan samar da ruwan sha na gaggawa a yankunan karkara

IMG 20250404 WA0012 720x430

Gwamnatin jihar Kano ta fara yunkurin gaggawa na magance matsalar karancin ruwan sha da ke addabar yankunan karkara, musamman a karamar hukumar Warawa.

Jaridar SolaceBase ta ruwaito cewa matakin ya biyo bayan umarnin da Gwamna Alhaji Abba Kabir Yusuf ya bayar bayan samun rahoton rashin ruwa a kauyukan Talawa, Ba’awa, da Dinyari da ke karamar hukumar Warawa.

A wata sanarwa da kwamishinan muhalli da sauyin yanayi Dr. Dahir M. Hashim ya fitar ranar Juma’a, ya ce gwamnatin ta danganta matsalar da tsananin zafi da matsanancin yanayi, wanda ya kafe magudanan ruwa da rijiyoyi, lamarin da ya sa al’ummomi da dama ke kokawa wajen samun tsaftataccen ruwan sha.

Dakta Hashim, wanda ya ziyarci yankunan da lamarin ya shafa, ya ce tuni jihar ta fara aikin samar da ruwan sha domin bayar da agajin gaggawa.

Ya yi nuni da cewa kawo yanzu an gina rijiyoyin burtsatse sama da 120 masu amfani da hasken rana a sassan jihar da suka hada da Falgore, Zangon Ranka, Sata, Hayyin Tagidadu, Kafin Agur, Kyallin Bula, da Mariri.

Da yake tabbatar wa al’ummar Kano, Kwamishinan ya jaddada kudirin gwamnati na samar da mafita na dogon lokaci da zai tabbatar da samun ruwa mai inganci da dorewa.

Ya kuma yi kira ga mazauna yankin da suka mallaki sabbin rijiyoyin burtsatse, inda ya ce tsaftataccen ruwa ba wai kawai yana hana cututtuka ba, har ma yana taimakawa wajen zuwa makaranta a tsakanin yara da kuma rage yawan cin zarafi ds mata da yara kanana ke fuskanta wajen neman ruwa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here