Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta haramta Hawan Sallah.
Rundunar ‘yan sandan ta alakanta hanarwar da matsalolin tsaro da kuma bukatar tabbatar da zaman lafiya.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP Ibrahim Adamu Bakori, ne ya sanar da dakatarwar a lokacin da yake zantawa da manema labarai a hedikwatar ‘yan sandan Bompai, ranar Juma’a.













































