‘yan sandan jihar Barno sun kama mutum 8 da ake zargin masu garkuwa da mutanene

Borno Police Commissioner Abdu Umar
Borno Police Commissioner Abdu Umar

Shugaban hukumar ‘yan sandan jihar Barno, Abdu Umar, ya ce sun kama mutane takwas da ake zargin masu garkuwa da mutanene.

Ya ce rundunan tasu ta kama wadanda ake zargin tsakanin watan March da kuma April.

Kumandan ya kara da cewa  yawan ci wadanda suka kama ana zargin su da hannu wajen garkuwa da mutane a Mubi da ke Adamawa, Taraba da kuma ita jihar ta Barnon.

Ya ce sun kama baban mai garkuwa da mutane, wanda ake zargin sa da sace Ibrahim Mohammed, ya yin da yake kokarin karbar kudin fansa, har naira miliyan biyu.

Ya kara da cewa dukkanin wadan ake zargi sun ansa lefin su, sanan ya bayyana cewa har yanzu hukumar tana neman wani kasurgumin mai garkuwa da mutane ruwa a jallo.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here