Yakin da ake yi da miyagun kwayoyi a Kano ya samu karin karfi da goyon bayan Kungiyar Tsoffin Yan Jaridu

Abba Kabir Yusuf 680x430

Kungiyar Tsoffin Yan Jaridu ta Jihar Kano ta bayyana goyon bayanta ga kafa kwamiti na musamman dan yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi (Kano State Special Task Force Against Drug Abuse and Trafficking) da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya kafa, inda ta bayyana wannan matakin a matsayin abin da dace kuma na yabo ga daya daga cikin manyan kalubalen zamantakewa da ke fuskantar jihar.

Shugaban rikon kwarya na Kungiyar, Alhaji Aminu Mahmud, ne ya bayyana goyon bayan yayin da yake jawabu kan kaddamar da kwamitin aiki na musamman, inda ya yi kira ga duk mutanen kirki, shugabannin al’umma, kungiyoyin fararen hula, cibiyoyin addini da sauran masu ruwa da tsaki su hada kai domin ganin an samu nasara.

A cikin wata sanarwa da daya daga cikin ‘yan kungiyar, Lamara Garba, ya fitar a ranar Laraba, ya ce kafa Kwamitin Aikin ya nuna jajircewar Gwamna wajen kare makomar matasan jihar Kano da kuma kiyaye dabi’u da tsarin zamantakewar al’umma.

“Matsalar yaduwar shan miyagun kwayoyi a tsakanin matasanmu na kara ta’azzara kuma abin damuwa ne. Kalubale ne da ke bukatar hadin kan gwamnati, iyalai, malamai, sarakuna, kafafen yada labarai da kowane dan kasa mai kishin al’umma. Ba wata hukuma daya kadai ba ce za ta iya magance wannan matsalar,” in ji shi.

Alhaji Mahmud ya tabbatar da cewa Kungiyar Tsoffin Yan Jaridun Kano za ta yi aiki tare da Kwamitin ta kowanne bangare domin tallafawa ayyukansa ta hanyar wayar da kai a koda yaushe, fada a ji da shiga harkokin yada labarai.

Ya ce ta hanyar kafa wannan Kwamitin, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya sake nuna jajircewarsa ga aikin gina Kano ta hanyar daukar matakai masu karfi wajen magance abubuwan da ke barazana ga lafiya, tsaro da kwazon matasa.

A cewarsa, yakin da ake yi da shan miyagun kwayoyi yana bukatar ci gaba da wayar da kai da kamfen din sauya halaye, yana mai jaddada cewa kafafen yada labarai na da muhimmiyar rawa wajen inganta kyawawan dabi’u da hana ayyukan da za su cutar da matasa.

Shugaban rikon kwarya ya bayyana cewa an kafa Kungiyar Tsoffin Yan Jaridun Kano ne a matsayin kungiya ta hadin kan kwararrun yan jarida domin horar da matasan yan jarida, inganta aikin jarida da dabi’un aiki, da kuma ba da gudummawa ga cigaban Jihar Kano da Najeriya baki daya.

Ya lura da cewa Kano, wadda ta samar da Shugabannin Kungiyar Yan Jaridu ta Kasa guda biyu da na kungiyar editoci ta kasa, ta dade tana bukatar kungiyar da za ta hada gogaggun tsoffin yan jaridanta domin amfanin bangaren da al’umma.

Alhaji Mahmud ya kara bayyana cewa kungiyar a halin yanzu tana shirin wasu shirye-shirye da kamfen din wayar da kai da ke da nufin wayar da kan mutane kan illolin shan miyagun kwayoyi da kuma inganta kasar shar da ba a ta’ammali da kwaya.

Ya bayyana kwarin gwiwarsa cewa idan aka ci gaba da hada kai tsakanin gwamnati, jami’an tsaro, kafafen yada labarai, kungiyoyin ‘yan kasuwa, kungiyoyin al’umma da jama’a, Kano za ta samu gagarumin ci gaba wajen rage shan miyagun kwayoyi tare da samar da al’umma mai lafiya da kwazo.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here