Gwamnan Kano ya nemi hukumar dake kula da manyan makarantu da ta tallafawa jami’o’in jihar Kano

IMG 20230711 WA0099 750x430
IMG 20230711 WA0099 750x430

Gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir yusuf ya nemi hukumar dake kula da manyan makarantu ta Najeriya da ta kara kokarin data take wajan taimakawa jami’o’i mallakin jihar kano domin kara inganta kowa da koyarwa a jami’o’in.

Jaridar solacebase ta rawaitu cewa gwamnan ya kai ziyara ne babbar shalkwatar hukumar dake Abuja domin neman hukumar ta kara kokarinta wajan taimakon jam’o’i mallakin jihar Kano.

A cikin wata sanarwa da babban sakataren yada labaran gwamnan jihar kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar a ranar Talata, ya ce Abba Kabir Yusuf ya bayyana hukumar ta TETFUND a matsayin jigo wajan kawo cigaba a hakar karatun al’umma.

“Duk wani kokarin da muke wajan ciyar da jami’o’in mu gaba, ba zai tasiri ba har in hukumar TETFUND bata samana hannu ba, muna da niyar kara gine gine a jami’o’in mu, taimaka musu wajan bincike da kuma bada horo ga malamai jami’ar.”

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here