Gwamnan jihar Katsina Umar Dikko Radda ya amince da nadin sabon shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta jihar, da kuma Karin wasu nade-naden a fannoni daban-daban na jihar.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da sakataren yada labaran gwamnan, Malam Ibrahim Kaula ya rabawa manema labarai a Katsina ranar Laraba.
Kamfanin Dillancin Labarai na kasa NAN, ya rawaito cewa a kwanakin baya ne gwamnatin Radda ta kafa hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Katsina.
Sabbin wadanda aka nada sun hada da; Mai Shari’a Lawal Garba mai ritaya a matsayin sabon shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Katsina, sai kuma Alhaji Usman Mamman Maska a matsayin shugaban hukumar kula da kananan hukumomi.
An kuma nada mambobin hukumar yaki da cin hanci ta jihar da suka hada da Dakta Jamilu Abdussalam a matsayin babban sakataren hukumar, da Malam Usman Dalhatu da Malam Surajo Doro sai Alhaji Abba Mato da Alhaji Kabir Aliyu-Maska da Alhaji Nafiu Kuringafa da kuma Alhaji Bello Danmusa.
Dikko Radda ya kuma yi kira ga wadanda aka nada din da su daidaita tunaninsu yayi dai-dai da tsarin gwamnatinsa wajen ganin an samar da ci gaba mai dorewa ga mutanen jihar Katsina.













































