Shugaba Bola Tinubu ya amince da nadin Malam Mohammed Abba Isa a matsayin babban mataimaki na musamman kan harkokin masu bukata ta musamman.
A wata sanarwa da mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai Ajuri Ngelale ya fitar a ranar Alhamis, yace nadin wani bangere ne na kudurorin shugaba Tinubu wajen tabbatar da cewa kowane bangare na al’umma ya samu wakilci a kunshin gwamnatinsa.
Sanatrwar ta bayyana cewa Malam Mohammed Abba Isa fitacce ne a cikin masu bukata na musamman wanda ya kwashe sama da shekaru 10 a fagen bayar da shawarwari a bangarorin da suka shafi al’amuran masu bukata ta musamman.

Sabon mai taimaka wa shugaban kasar dai ya kammala karatunsa na digiri ta farko a fannin nazarin dabarun mulki da gudanarwa ne a jami’ar Maiduguri inda ya ci













































