Atiku ya yi zargin ana shirya wata sabuwar makarkashiya don hana ADC shiga zaben 2027

former Vice President Atiku Abubakar 750x430

Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar ya yi zargi cewa akwai sabon shiri da wasu da ba a bayyana sunayen su ba a cikin gwamnati mai mulki da ke yi domin hana jam’iyyar ADC shiga zaben 2027, yana mai gargadin cewa duk wani yunkuri na hana jam’iyyar adawa shiga zabe Babbar illa ce ga dimokuradiyyar Najeriya.

Atiku, wanda shi ne dan takarar shugaban kasa na ADC, ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da Mataimakin sa na musamman a bangaren sadarwa, Phrank Shaibu, ya fitar a ranar Litinin. Ya ce ya samu bayani mai inganci da ke nuna cewa ana shirya wasu dabaru na siyasa da na shari’a domin hana jam’iyyar shiga takara.

A cewarsa, wannan yunkurin da ake zargi wani bangare na yin wani babbar shiri na raunana jam’iyyun adawa da hana ‘yan Najeriya damar zabar shugabansu a bayyane.

“Mun san cikakken shirinsu. Yayin da suke neman kirkirar da rudani a cikin jam’iyyun adawa, mun san cewa abin da suke so shi ne ADC saboda ita ce mafi inganci kuma zabin al-umma,” in ji Atiku.

Ya yi kira ga ‘yan Najeriya, ba tare da la’akari da jam’iyyarsu ba, su yi adawa da abin da ke bayyana a matsayin yunkurin jam’iyyar APC mai mulki na tantance wanne jam’iyyar adawa za a baiwa damar shiga zabe.

“Sakon mu ga APC da kuma wadanda ke shirya makirci a boye shi ne, kuna iya yin makirci, amma ba za ku yi nasara ba. Idan APC da gaske tana da kwarin gwiwa kan shaharar ta, me ya sa take jin tsoron ADC haka?” in ji shi.

Duk da cewa ya tabbatar da cewa ba za a aiwatar da wannan shiri da ake zargi ba, Atiku ya ce abubuwan da suke faruwa a kwanakin nan na siyasa sun sa zai yi wuya a yi watsi da irin wadannan gargadi.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here