‘Yan Sanda sun fara neman mutanen da ake zargi kan mutuwar malama da aka yi wa duka saboda ladabtar da dalibi a Kogi

Police olopa sabo

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kogi ta fara bincike kan mutuwar wata ma’aikaciyar makaranta, Maryam Usman, sakamakon wani hari da ake zargin an kai mata a Makarantar Brains Minds Nursery and Primary School dake Ugbamaka, karamar hukumar Olamaboro.

A cewar Jami’ar hulda da jama’a ta rundunar, ASP Afusat Oyiza Salihu, ta bayyana. Ta bayyana ce an kai rahoton faruwar lamarin ga Ofishin ‘Yan Sanda na Olamaboro a ranar 25 ga watan Yunin 2026, a matsayin karar kisan kai da aka yi da niyya.

“Binciken farko ya nuna cewa a ranar 18 ga watan Yuni 2026, an zargi wani suna Abdullahi Ishaka da mata biyu da shiga makarantar in da suka farmaki Maryam Usman mai shekaru 30, saboda hukuncin da ta yi wa wani dalibi.

“A cewar rahoton, wadda abin ya shafa ta samu munanan raunuka a lokacin. Da farko an kaita asibiti a Ugbamaka domin agajin farko kafin a mika ta zuwa Asibitin Iko-Ojo da ke Okpo domin karin kulawa. Sai dai ta mutu a ranar 25 ga watan Yuni sakamakon raunukan.”

Bayan samun rahoton, jami’an ‘yan sanda sun ziyarci wurin da lamarin ya faru da kuma gidan marigayiyar domin gudanar da bincike da rubuta bayanan.

Hukumomi sun ce an shirya kai gawar zuwa Babban Asibitin Ankpa, don binciken likitoci.

An ce masu laifin sun tsere kafin zuwan jami’an tsaro. Rundunar ‘Yan Sanda ta ce ana ci gaba da kokarin kama su, inda ta kara da cewa da zarar an kama su, za a mika shari’ar zuwa Sashen Binciken Manyan Laifuka na Jihar (SCID) domin cikakken bincike cikin sirri.

Rundunar ta sake jaddada kudirin ta na tabbatar da cewa an gurfanar da duk wadanda ke da hannu a lamarin.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here