Dangote ya karya farashin dizel a Najeriya

Dangote, dizel, farashi. najeriya
Matatar mai ta Dangote ta sanar da ƙara rage farashin dizel daga Naira 1,200 zuwa Naira 1,000 duk lita ɗaya. Ƴan makonnin da suka gabata, lokacin da matatar...

Matatar mai ta Dangote ta sanar da ƙara rage farashin dizel daga Naira 1,200 zuwa Naira 1,000 duk lita ɗaya.

Ƴan makonnin da suka gabata, lokacin da matatar ta soma aiki, kamfanin yana sayar da farashin dizel a kan naira 1,200 duk lita guda.

Hakan na nufin an yi ragin fiye da kashi 30 cikin 100 daga farashin da ake sayar da dizel ɗin a baya kimanin Naira 1,600 kowace lita.

Karin labari: KEDCO ta saka hannun jari na Naira Biliyan 1.2 don fadada sadarwa

Matatar ta ce muhimmin ragin da aka yi kan farashin na dizel zai yi tasiri sosai a ɓangaren tattalin arziki tare da rage hauhawar farashin da ake fuskanta a Najeriya.

Matatar Dangote ta soma gudanar da harkokinta ne da sayar da man jirgi da kuma na dizel.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here