Gwamnatin tarayya ta amince da ƙarin albashin ‘yan sanda

FEC KN A
FEC KN A

Majalisar zartaswa ta tarayya ta amince da sake duba tare da inganta albashin ‘yan sanda da kashi 20 cikin 100.

Ministan harkokin ‘yan sanda, Maigari Dingyadi ne ya bayyana hakan a ranar Laraba bayan kammala taron majalisar zartarwa ta tarayya wanda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranta.

A cewar ministan, ana sa ran sabon tsarin zai fara aiki daga watan Janairun 2022.

Dingyadi ya ci gaba da cewa, wannan lamarin ya biyo bayan bukatun da masu zanga-zangar EndSARS suka gabatar a shekarar 2020, wanda ya shafi inganta jin dadin jami’an ‘yan sanda.

Shugaba Buhari ya yi alkawarin cewa za a inganta albashin yadda ya kamata don ci gaba da wanzar da zaman lafiya a kasar.

FEC ta kuma amince da fitar da Naira biliyan 13.1 don biyan wasu alawus bayan mutuwar ma’aikata 5,472 da inshora daga 2013 zuwa Agusta 2021.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here