Gwamnonin da aka zaba a jam’iyyar PDP a ranar Lahadin da ta gabata sun yi wata ganawar sirri da wasu tsofaffin gwamnonin inda suka tattauna al’amuran jam’iyyar da suka hada da rikicin shugabancin da take ciki.
Taron kungiyar Gwamnonin PDP (PDP-GF), wanda aka gudanar a masaukin Gwamnan Bauchi da ke Abuja, ya samu jagorancin Shugabanta, Gwamna Bala Mohammed na Jihar Bauchi.
Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ya ruwaito cewa gwamnonin da suke a taron sun hada da na jihohin Enugu, Zamfara, Plateau, Taraba, Adamawa, Osun da kuma Oyo.
Haka kuma ana sa ran za a tattauna a taron har da taron kwamitin zartarwar jam’iyyar na kasa da za a yi a ranar 27 ga watan Mayu.

NAN ta ruwaito cewa, wadanda suka halarci taron sun hada da mukaddashin shugaban jam’iyyar na kasa, Urmar Damagum, sakataren kwamitin amintattu (BoT) da tsohon gwamnan jihar Kaduna, Ahmed Makarfi, da kuma tsohon shugaban majalisar dattawa, Sanata Bukola Saraki.
Haka kuma a wajen taron akwai ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike, wanda ya isa da misalin karfe 9.25 na dare.

Sauran sun hada da Sanata Aminu Tambuwal, Sule Lamido, Okezie Ikpeazu, Samuel Ortom, Gabriel Suswam, Seriake Dickson, Sam Egwu, Liyel Imoke, Achike Udenwa, Olagunsoye Oyinlola, Adamu Muazu da Idris Wada.

Mambobin kwamitin ayyuka na jam’iyyar PDP na kasa da suka hada da sakataren kungiyar na kasa Umar Bature da kuma mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin shari’a, Kamaldeen Ajibade, sun halarci taron. (NAN













































