Gwamnatin Kano ta kara yawan jami’an da za ta tura aikin Hajjin 2025 – Gwamna Yusuf

WhatsApp Image 2025 02 06 at 20.52.14 750x430

Gwamnatin jihar Kano ta kara yawan jami’an jihar da ya ba su kujerar aikin hajji domin tabbatar da yin hidima ga alhazai a kasar Saudiyya ta fuskar jagoranci, kiwon lafiya, da tallafi.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya sanar da hakan ne a ranar Lahadin da ta gabata yayin bikin rufe bitar alhazai na aikin hajjin 2025 a Kano.

“Mun tattara tawagogi masu kwazo domin biyan bukatun alhazanmu, tun daga filin jirgin sama har zuwa masauki, da kuma tsawon zamansu a kasar Saudiyya, burinmu shi ne mu sanya aikin hajjin bana ya zama mafi sauki da kwanciyar hankali a tarihin Kano,” inji shi.

Gwamnan ya bayyana cewa zai jagoranci tawagar jihar zuwa kasar Saudiyya domin gudanar da aikin hajjin shekarar 2025.

Ya kuma jaddada cewa yin aikin Hajji ba tafiya ce ta addini kawai ba, a’a ibada ce da ke bukatar nuna ɗa’a da tarbiyya.

Karin karatu: Tawagar ƙwararru ta NAHCON ta tashi zuwa Makkah domin kaddamar da aikin Hajji

Ya kuma gargadi alhazai da su kiyaye bata sunan jihar, inda ya bukaci alhazai musamman matasa da mata da su rika gudanar da ayyukansu cikin ladabi da mutuntawa da kamewa duk tsawon zamansu a kasa mai tsarki.

Ga matasan mu, ina kira gare ku da ku guji duk wani abu da zai iya kawo wa jiharmu rashin mutunci ko bala’i. Su kuma matan mu, ku tuna cewa matan Kano an san su da ladabi. Ku wakilce mu da alfahari, ku mutunta kanku, kuma ku kare martabar al’adunmu da addininmu,” inji shi.

Gwamna Yusuf ya kuma yi gargadin a guji shan miyagun kwayoyi da lalata a lokacin aikin hajji, yana mai cewa irin wadannan ayyuka sun saba wa alfarmar aikin Hajji da koyarwar Musulunci.

A nasa bangaren, Shugaban Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kano, Alhaji Lamin Rabi’u Danbappa, ya ce an shirya jimillar maniyyata 3,335 daga jihar don tafiya aikin Hajjin shekarar 2025.

Ya ce hukumar alhazai ta kasa NAHCON ya zuwa yanzu ta bayar da biza ga maniyyatan Kano guda 2,988, yayin da 347 ke kan aiki.

“Shugabannin NAHCON sun tabbatar mana da cewa sauran biza za su kasance a shirye daga yau zuwa gobe,” inji shi.

Alhaji Danbappa ya kuma bayyana cewa hukumar jin dadin alhazai ta jihar Kano ta biya jimillar Naira biliyan 24.5 ga hukumar NAHCON domin jigilar maniyyata da jin dadin alhazai.

Ya kuma bayyana cewa za a fara gudanar da jigilar aikin Hajji a hukumance a ranar Talata 13 ga watan Mayu, inda jirgin farko zai yi jigilar maniyyata 400 daga kananan hukumomin Tudun Wada, Doguwa, Bebeji, Garun Mallam, da Rimin Gado.

Ya kuma bukaci dukkan maniyyatan da su bi ka’idojin da hukumomin Najeriya da na Saudiyya suka gindaya don tabbatar da gudanar da aikin hajji cikin sauki da nasara.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here