Gwamnatin tarayya ta ce zata budi sabowar jami’ar sufuri da aka kafa a jihar Katsina a watan Satumba na shekarar 2022.
Ministan harkokin sufuri, mista Mu’azu Sambo ne ya bayyana hakan yayin ziyarar aiki da ya kai jami’ar dake Daura ranar alhamis.
Ya yin ziyarar aikin ministan ya ce aikin gina jami’ar da aka fara shi bara, a yanzu haka an kammala kaso 60 cikin 100.
A nasa bangaran sakataran hukumar ta sufuri, Dakta Magdaline Ajani, ya ce bayan an kammala ginin jami’ar za’a mikata hannun ‘yan chana zuwa tsawan shekaru biyu.
Ajan ya kara da cewa NUC zata bada dokokin gudanarwa ga jami’ar kamar ko wace jami’a a kasa baki daya.













































