Dalilin da yasa muka karɓe lasisin gudanar da duk wasu makarantu masu zaman kansu a jihar Plateau-kwamishina

Simon Lalong
Simon Lalong

Kwamishinan ilimi na jihar Plateau, Mista Elizabeth Wapmuk, ya ce gwamnatin jihar ta karɓe lasisin gudanar da duk wasu makarantu masu zaman kansu a fadin jihar baki daya.

Wapmuk ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na kasa NAN, ranar Juma’a a Jos cewa, gwmnatin jihar ta yanke hukuncin ne bisa gano sama da makarantu 5,000 masu zaman kansu a jihar na gudanar da aikin su ba tare da sahalewar gwamnati ba.

Solacebase ta rawaitu cewa hukumar ilimi ta jihar na kokarin sabunta lasisin makarantu masu zaman kan su, tun daga karamar firamare, babbar firamare, karamar sakandare da kuma babbar sakandare na jihar.

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here