Bin diddigin Kasafin Kudi: wata gidauniya ta bibiyi sama da Ayyukan Mazabu Dubu 16 a Kananan Hukumomi 583

signpost of abandoned project 2 640x430 1
signpost of abandoned project 2 640x430 1

Gidauniyar dake bin diddigin ayyukan mazabun Kasar nan wato Budget Foundation, ta ce ta binciki ayyukan mazabu Dubu 16 da 213 a kananan hukumomi 583 daga cikin 774 na kasar nan.

Kwararre Kan harkokin Kasafin Kudi na Gidauniyar, Mista Henry Omokhaye, ne ya bayyana hakan a Lokoja yayin wani taron horaswa na kwanaki 2 da gidauniyar Stallion Times da ke tallafawa gidauniyar MacArthur, ta shirya a ranar Alhamis.

Masanin kasafin kudin, wanda ya yi magana kan maudu’in: “bin diddigin Kasafin Kudi: tare da Fahimtar yadda aka gudanar da Ayyukan Mazabu,” ya jaddada muhimmancin bibiyar kasafin kudi tare da sanar da Yan Kasa ta hanyar amfani da kafafen yada labarai.

Omokhaye ya ce an gudanar da binciken ne a yankuna Dubu 11 da 17 a cikin jihohi 33 na kasar nan tare da gudanar da taron jin ra’ayoyin al’umma har sau Dubu 9 da 56 game da ayyukan mazabu.

Ya ce a gaskiya hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta ICPC a shekarar 2019 ta kafa wani shiri Mai suna CPTG Initiative wanda ya kunshi wakilai daga ofishin kasafin kudi da Ofishin Akanta-Janar, da kungiyoyin fararen hula da kuma kafafen yada labarai don sanya ido kan ayyukan na mazabu.

A cewarsa, matakin farko shi ne tantance aikin mazabar, da ziyartar wurin da za a yi, a Kuma sanar da al’umma ta kafar Internet da kuma taimaka wa ‘yan Kasa su rubutawa wakilansu na majalisar dokokin kasa.

Ya ce kayan aikin bin diddigin sun hada da kyamarori da na’urar GPS, da sauransu.

Masanin ya kuma yi gargadin cewa rashin sanya ’yan kasa wajen bin diddigin kasafin kudi da bayar da rahoto na iya haifar da rashin aiwatar da ayyuka ko watsi da ayyukan ma baki daya.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here