Bazoum ya karrama Aliko Dangote

DSC1292 750x430 1
DSC1292 750x430 1

Shugaban Kamfanin Dangote, Alhaji Aliko Dangote ya samu lambar yabo daga Shugaban Jamhuriyar Nijar, Mohamed Bazoum a birnin Yamai.

An bashi lambar yabon ne don nuna godiya ga ayyukan da yake yi a Jamhuriyar Nijar da kuma karramawa ga kwazonsa na kasuwanci da kuma ayyukan alheri.

Idan za a iya tunawa gidauniyar sa, Mai suna Aliko Dangote Foundation (ADF) ta shiga bangarori daban-daban domin inganta harkokin kiwon lafiya da rigakafi na yau da kullum a jamhuriyar Nijar da makwabtanta wato Najeriya da Chadi.

Gidauniyar Aliko Dangote da BMGF sun taka muhimmiyar rawa a tarihin hukumar Lafiya ta Duniya.

Yankuna uku na Diffa, Maradi da Zinder suna da iyaka da Arewacin Najeriya kuma a hade kusan kashi 28% na fadin kasar Nijar da kuma kashi 40% na al’ummar kasar sun amfana da ayyukan gidauniyar.

A wani labarin kuma, Gidauniyar Aliko Dangote tare da gidauniyar Bill & Melinda Gates (BMGF) sun rattaba hannu kan wata yarjejeniya da gwamnatin Jamhuriyar Nijar kan hadin gwiwar inganta shirin da aka fadada a kasar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here