Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya zagaya gonaki 10 a fadin kananan hukumomi hudu dake cikin birnin Maiduguri da Jere da Mafa da Dikwa domin sa ido kan ayyukan noma.
A yayin ziyarar da ba a shirya ba, Farfesa Zulum, ya tattauna da manoma, inda ya tambaye su matsalolin da suke fuskanta domin a magance su.
Da damina ta samu, an ga akasarin manoma suna ciyawa da shuka a mafi yawan filayen noma lokacin da gwamnan ya kai musu ziyarar.
Zulum ya bayyanawa manoman cewa sabanin sauran jihohi, jihar Borno ta gaza shigowa tare da ware wa manoma takin NPK saboda akwai dokar hana fita da gwamnatin tarayya ta yi ta ofishin mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro.

Ya ce a dalilin haka ne ya ba da umarnin rarraba kayan amfanin gona da taraktoci ga manoma a sassan yankin Sanatoci uku na Jihar Borno: da suka hadar da Borno ta Tsakiya, da ta Kudu da Kuma ta Arewa.
Ya yi alkawarin inganta aikin noma musamman ci gaba da karfafa ayyukan noma da sauran kungiyoyin tsaro don ci gaba da ayyukan noma cikin koshin lafiya a fadin jihar Borno.













































