Zaben Osun: APC ta yi watsi da sakamakon INEC, ta bayyana dalilai

Adeleke AND Oyebamiji 750x430

Kungiyar yakin neman zaben gwamna ta jam’iyyar APC a Jihar Osun ta ki amincewa da sakamakon zaben gwamna na ranar 15 ga Agusta, tana mai cewa Gwamna Ademola Adeleke bai samu mafi yawan ingantattun kuri’un da aka kada a zaben ba.

Daraktan Janar na yakin neman zaben APC, Oluwole Oke, ne ya bayyana hakan a wata hira da Arise News a ranar Litinin, inda ya bayyana dalilin da yasa jam’iyyar ba ta taya Adeleke murna kan sake cin zaben ba.

Oke ya ce jam’iyyar ba ta yarda da sanarwar da Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta yi ba, kuma sun fara nazarin kayan zabe kafin su yanke shawarar matakin da za su ɗauka na gaba.

Ya ce “Ba mu yarda da sanarwar INEC ba. Wannan ita ce matsayarmu a yanzu. Muna ganin bai samu mafi yawan ingantattun kuri’u ba.”

A cewarsa, kungiyar yakin neman zaben APC ba za ta bari a tilasta mata amincewa da sakamakon ba har sai sun kammala cikakken nazari kan yadda aka gudanar da zaben.

“Kamar yadda na fada muku, abin da muke yi, har ma don tarihi na gaba, shi ne mu gudanar da cikakken nazari kan duka tsarin, sannan mu sanar da matsayarmu.
Ba za mu mika wuya ga matsin lamba da gaggauta taya Sanata Ademola Adeleke murna ba,” in ji Oke.

INEC ta ayyana Adeleke na jam’iyyar Accord a matsayin wanda ya ci zaben bayan ya samu kuri’u 511,067, inda ya doke dan takarar APC, Bola Oyebamiji, wanda ya samu kuri’u 444,815.
Dan takarar ADC, Najeem Salaam, ya zo na uku da kuri’u 17,180.

Sakamakon ya nuna Adeleke ya samu nasara a Kananan Hukumomi 19, yayin da Oyebamiji ya yi nasara a 11. Adeleke ya yi nasara da bambancin kuri’u 66,252.

Ko da yake Shugaba Bola Tinubu ya taya Adeleke murna bayan sanarwar sakamakon, Oke ya ce matsayin kungiyar yakin neman zaben APC ya bambanta saboda suna da hankali kan nazarin abubuwan da suka faru a zaben.

Ya ce jam’iyyar ta fara bibiyar zaben kuma ta umarci duk wakilan jam’iyyar a fadin jihar da su kawo kwafin takardar EC8A, B da C zuwa sakatariyar jam’iyyar domin dubawa.

“Mun fara aikin bibiya. Mun umarci duk wakilan mu da su kawo kwafin takardar EC8A, B da C zuwa sakatariya domin nazari. Muna bukatar binciken kayan,” in ji Oke.

Shugaban ya ce nazarin zai hada da yadda aka gudanar da zaben da kuma abubuwan da suka faru kafin zaben, ciki har da bin Dokar Zabe da sauran dokoki.

Ya kuma nuna cewa jam’iyyar na iya bin hanyar shari’a idan binciken su ya nuna akwai hujja.

A cewar APC, tsarin zabe bai tsaya a sanarwar sakamako ba. Zai iya ci gaba har zuwa Kotun Zabe, Kotun Daukaka Kara da Kotun Koli idan ya cancanta.

“Har sai mun kammala hakan kafin tsayar da matsayarmu, ba za mu iya ci gaba da cewa wani abu ba a kan haka,” in ji Oke.

Jam’iyyar ta kuma roki magoya bayanta da jama’a da su ba ta damar kammala kimanta zaben kafin ta sanar da matakin da za ta dauka na gaba.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here