Zargin Almundahana:Kotu tace akwai tambayoyin da Lamido zai amsa a gabanta

Sule Lamido
Sule Lamido

Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Abuja ta yanke hukuncin cewa tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido da sauran wadanda ake tuhumarsu, za su amsa tambayoyi game da zargin karkatar da kudade har Naira miliyan 712.

Hukumar EFCC, na tuhumar Sule Lamido tare da ‘ya’yansa biyu – Aminu Sule Lamido da Mustapha Sule Lamido.

Sauran wadanda ake tuhuma a karar sun hada da Aminu Wada Abubakar, da abokan kasuwancin Lamido da Kuma wasu kamfanoni hudu, wadanda suka hada da Bamaina Company Nigeria Limited da Bamaina Aluminum Limited sai Speeds International Limited da kuma Batholomew Darlington Agoha.

Wadanda ake tuhumar suna fuskantar tuhume-tuhume 37.

Bayan da EFCC ta rufe karar, Lamido ya shigar da wata kara inda ya ce shaidun da masu gabatar da kara suka bayar ba su bayyana wasu dalilai a kansa ba.

Sai dai kuma mai shari’a Ijeoma Ojukwu ya yi watsi da karar da Lamido ya shigar a gaban kotun a ranar Litinin.

Alkalin kotun ya umarce shi da ya bude kariyar tasa a ranar 8 ga watan Nuwamba.

An karanta daya daga cikin tuhume-tuhumen kamar haka: “Kai Alhaji Sule Lamido (a lokacin da kake Gwamnan Jihar Jigawa a Najeriya), a ranar 15 ga Disambar 2008, a asusunka mai sunan Bamaina Holdings wanda ke bankin Unity Plc. Kano, an sanya kudin da ya kai Naira Miliyan Goma sha hudu, da dubu Dari Takwas da Hamsin, wanda kamfanin Dantata & Sawoe Construction Company Nigeria Limited, ya biya, a bankin Intercontinental Wanda yanzu ya zama Access Bank, da Chakin kudi mai Lamba 00000025, wanda hakan ke nuni da cewar wadannan kudade haramtattu ne domin Kuwa kun yi amfani da matsayin ku na mahukunta kuna bada kwangila ga kamfanonin da kuke da alaka da su.

Gwamnatin jihar Jigawa ta ba da kwangiloli da nufin boye kurakurenta, wadda hakan laifin ne da ya sabawa sashe na 14(1) (a) na dokar hukunta masu samarwa kansu kudi ta haramtacciyar hanya, ta Shekarar 2004 za kuma a hukunta duk wanda aka samu da laifin karkashin sashe na 14(1) na dokar.”

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here