Kungiyar Masu Dillancin Man Fetur ta Najeriya (PETROAN) ta ce Kamfanin Matatar Mai na Fatakwal bai fitar da wani sabon farashin saye na mai ba.
Dr Billy Gillis-Harry, Shugaban PETROAN na kasa ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa a ranar Laraba.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa matatar mai da ke karkashin kamfanin ‘Nigerian National Petroleum Company Ltd. (NNPC Ltd.)’ a ranar Talata ta fara aikin tace man fetur na farko tun bayan lalacewar da tai.