Gidan Talabijin na Africa Independent Television (AIT) ya mika uzuri ga hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) kan wani rahoto da ke cewa jami’anta sun mamaye majalisar dokokin jihar Legas a ranar 17 ga watan Fabrairu.
Uzurin wanda aka bayar a yayin wani shirin sa na News Hour kai tsaye, ya zo ne bayan da hukumar DSS ta yi barazanar daukar matakin shari’a a kan AIT, da kuma gudanarwar gidan Talabijin na Channels a kan “rahoto na karya da suka yaɗq.
Hukumar ta DSS ta kuma bukaci kafafen yada labarai da su janye labarin tare da neman afuwar jama’a.
A cikin faifan bidiyo da suka yi ta yawo a shafukan sada zumunta a ranar Litinin, an ga jami’an DSS na kokawa da ‘yan majalisar dokokin jihar.
A cewar hukumar ta DSS, rahoton ya yi zargin cewa jami’anta sun yi yunkurin hana ‘yan majalisar dokoki ciki har da Mojisola Meranda, shugabar majalisar shiga zauren majalisar.
Bayan nan dai bayanai sun nuna cewa mukaddashin magatakardar hukumar ya gayyaci hukumar DSS a hukumance domin ta taimaka wajen tabbatar da zaman lafiya biyo bayan bayanan sirri da aka samu cewa hambararren kakakin majalisar, Mudashiru Obasa, na shirin komawa bakin aiki ranar 18 ga watan Fabrairu, matakin da majalisar ke ganin yana da hadari ga tsaro.
A cikin uzurin da ta baiwa DSS, AIT ta amince da cewa bayanan da ta waya basu da inganci kuma ba da niyya ta yi ba.
“Manufarmu ba ita ce mu bata ko kunyata hukumar DSS ba, hukumar da muke mutunta muhimmanci da rawar da take takawa wajen kare al’ummarmu, amma rahotannin da muka samu sun samo asali ne daga shaidun gani da ido da muka samu daga majiyoyin da ke akwai a majalisar dokokin jihar Legas.
Karin karatu:Hukumar DSS ta musanta kai hari fadar Sarkin Kano
Shi ma gidan talabijin na Channels, a ranar Juma’a, ya bayar da uzuri a cikin shirinsa na siyasa, wanda Seun Okinbaloye ke gabatarwa, inda tsohon mataimakin shugaban hukumar DSS, Muhammed Ngoshe, ya kasance bako.
Okinbaloye ya bayyana cewa, an yi wa lamarin mummunar fassara da faifan bidiyo na farko da ke nuna hoton ‘yan majalisar da suka firgita da kasancewar jami’an DSS, wanda ke nuna cewa jami’an DSS sun mamaye su.
Sai dai daga baya an bayyana cewa magatakardan majalisar shi ya bukaci hukumar ta DSS a hukumance domin samun kariya.
Da yake mayar da martani, Ngoshe ya nuna jin dadinsa ga janyewar da suka yi da kuma amincewa da rawar da hukumar ta DSS ke takawa.
Idan dai za a iya tunawa, hukumar ta DSS ta yi barazanar daukar matakin shari’a a kan kafafen yada labaran biyu, inda ta zarge su da buga rahotannin karya da kuma na bogi.