Hukumar DSS ta musanta kai hari fadar Sarkin Kano

DSS, hukumar, masarautar, kano, rano, gaya, karaye, bichi, tinubu
Hukumar ‘yan sandan farin kaya (DSS) a ranar Alhamis ta musanta rahotannin da wasu kafafen yada labarai ke yadawa na cewa ta mamaye fadar Sarkin Kano, inda...

Daga: Sunusi A. Dantalata Fagge

Hukumar ‘yan sandan farin kaya (DSS) a ranar Alhamis ta musanta rahotannin da wasu kafafen yada labarai ke yadawa na cewa ta mamaye fadar Sarkin Kano, inda ta ce ba gaskiya ba ne.

Daraktan DSS na jihar, Muhammad Alhassan ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Kano.

Karin labari: Da Dumi-Dumi: Majalisar dokokin Kano ta amince rushe sabbin Masarautu

Alhassan ya ce hukumar ta DSS ta tura jami’anta zuwa fadar ne kawai a wani bangare na shirin tsaro na ziyarar da uwargidan shugaban kasa, Misis Oluremi Tinubu ta kai wa Sarkin.

Ya ce, duk da haka, an janye ma’aikatan ne, biyo bayan dage ziyarar da Sarkin ya yi a garin.

Ya ce babu gaskiya a cikin rahoton da ke cewa jami’an DSS sun kai farmaki fadar sarkin kan lamarin da ke faruwa a fadar gwamnatin jihar.

Karin labari: An tsaurara matakan tsaro a zaman majalisar dokoki kan gyaran masarautun Kano

Ya bukaci ‘yan Najeriya da su yi watsi da rahoton na karya, wanda ya ce an yi shi ne don haifar da tashin hankali da ba su dace ba.

A ranar Alhamis ne Majalisar Dokokin Jihar ta soke dokar Majalisar Masarautar Kano ta 2019, inda ta rusa masarautun Bichi, Gaya, Karaye, da Rano.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here