Da Dumi-Dumi: Majalisar dokokin Kano ta amince rushe sabbin Masarautu

Majalisar, Dokokin, Kano, bichi, gaya, karaye, rano, madari, ganduje, masarautu, rushe, soke
Majalisar dokokin jihar Kano ta amince da dokar soke masarautun Kano bayan kammala karatu na uku. Dokar ta soke kafa sabbin masarautu guda 5 a jihar...

Daga: Sunusi A. Dantalata Fagge

Majalisar dokokin jihar Kano ta amince da dokar soke masarautun Kano bayan kammala karatu na uku.

Dokar ta soke kafa sabbin masarautu guda 5 a jihar.

Duk ofisoshin da aka kafa a karkashin dokar da aka soke an kebe su da sabon kudirin.

Haka kuma duk hakimai da aka daukaka ko aka nada a karkashin dokar da aka soke za su koma kan mukamansu na baya.

Karin labari: HOTO: Al’umma a Kano sun koka matuka kan masu hakar yashi da ma’adanai

Shugaban masu rinjaye kuma memba mai wakiltar mazabar Dala, Lawan Hussaini Chediyar Yan Gurasa ne ya dauki nauyin majalisar dokokin jihar Kano kan (gyara mai lamba 2) ta 2024.

Dokar wadda ta kafa sabbin masarautu guda biyar ta kasance tsohon gwamna Abdullahi Umar Ganduje ne ya fara sanya hannu a kan dokar a ranar 5 ga watan Disamba, 2019.

Gwamnan ya amince da gyara dokar a ranar 14 ga Oktoba, 2020 tare da sanya hannu kan wani gyara a ranar 11 ga Afrilu, 2023.

Karin labari: An tsaurara matakan tsaro a zaman majalisar dokoki kan gyaran masarautun Kano

Sashi na 3 (1) na dokar ya kafa masarautu daban-daban guda biyar da suka hada da Kano, Bichi, Rano, Gaya da Karaye, tare da Karaye suna da ƙananan hukumomi takwas kowacce, yayin da masarautun Bichi da Gaya suke da ƙananan hukumomi 9 kowannensu, Masarautar Rano tana da ikon mallakar fiye da ƙananan hukumomi 10 daga cikin 44 na kananan hukumomi a jihar.

Lokacin da aka tsige Sarki Muhammadu Sanusi, wanda ya jagoranci majalisar a ranar 9 ga Maris, 2020, an yi wa dokar gyaran fuska a karanta: “Akwai shugaban majalisar wanda zai zama sarkin Kano”.

Karin labari: Hukumar INEC ta karbi wasika daga mazabu na sake kiran dan majalisar wakilai

Sashi na 12 ya tanadi cewa gwamna na iya sanya mukamin sarki a matsayi na daya, ko na biyu, ko na uku bisa amincewar majalisar dokoki.

Wani babban jami’in majalisar, wanda bai so a ambaci sunansa ba, ya ce “babu wani tanadi da zai hana majalisar yin gyara ga doka.”

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here