Daga: Sunusi A. Dantalata Fagge
Jami’an tsaro na ‘yan sanda da na NSCDC sun mamaye wasu muhimman wurare a zauren majalisar dokokin jihar Kano, a ranar Laraba, yayin da ‘yan majalisar suka fara gyaran dokar majalisar masarautun jihar da ta kafa masarautu biyar.
Gyaran dokar Masarautar Kano (gyara mai lamba 2) ta 2024 (1445AH) wanda shugaban masu rinjaye kuma memba mai wakiltar mazabar Dala, Lawan Hussaini Chediyar Yan Gurasa ya dauki nauyin yi.
An bukaci ‘yan jaridar da suka zo domin gudanar da ayyukan na ranar da su bayyana kansu kafin a ba su izinin shiga yayin da duk hanyoyin da ke shiga harabar majalisar suka toshe.
Karin labari: HOTO: Al’umma a Kano sun koka matuka kan masu hakar yashi da ma’adanai
Dokar Majalisar Dokokin Jihar Kano ta 2019 wacce ta kirkiro sabbin masarautu guda biyar tsohon Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ne ya fara sanyawa hannu a ranar 5 ga watan Disamba, 2019.
Gwamnan ya amince da gyara dokar a ranar 14 ga Oktoba 2020 tare da sanya hannu kan wani gyara a ranar 11 ga Afrilu 2023.
Sashi na 3 (1) na dokar ya kafa masarautu guda 5 na Kano wanda ya hada da Bichi da Rano da Gaya da Karaye da kuma Kano suna da kananan hukumomi 8 kowacce, yayin da Masarautar Bichi da Gaya ke da kananan hukumomi 9 kowacce, sai kuma Rano. Masarautar tana da iko sama da kananan hukumomi 10 daga cikin kananan hukumomi 44 da ke cikin jihar.
Karin labari: Da Dumi-Dumi: Majalisar dokokin jihar Kuros Riba ta tsige kakakinta
Sashi na 4 na dokar ya kafa majalisar sarakunan jihar wanda ya hada da sarakuna 5 da sakataren gwamnatin jiha da kwamishinan kananan hukumomi da shugabanni 5 kowanne daya daga masarautu da kuma sarakuna 10 da wakilai daga ‘yan kasuwa da sauransu.
Sashi na 5 ya tanadi shugabancin majalisar sarakuna wadda za ta rika karba-karba a tsakanin sarakuna.
Dokar ta kuma bayyana cewa inda sarakunan suka kasa tantance wanda zai gaje shi a cikin kwanaki 3 gwamna da kansa na iya nada irin wannan daga cikin masu gadon sarauta kamar yadda ya ga dama.
Karin labari: Gwamnan Kano ya nemi haɗa kai da kasar Netherland kan habaka noma da dakile illolin sauyin yanayi
Sashi na 12 ya tanadi cewa gwamna na iya sanya mukamin sarki a matsayi na daya, na biyu, da na uku, bayan amincewar majalisar dokokin jihar.
Sashi na 13 ya tanadi cewa gwamna bayan bincike da tuntubar majalisar sarakuna zai iya tsige irin wannan sarki idan ya gamsu cewa ana bukatar tsige shi bisa ga al’ada ko kuma da gangan sarkin ya kasa halartar tarukan majalisar har tsawon kwanaki 3 a jere. ba tare da wani uzuri mai inganci ba ko kuma ya aikata mummunan aiki ko cin zarafin ofishi ko fasikanci.
Sai dai duk da dambarwar da ta biyo baya a zaman majalisar na yau, shugaban marasa rinjaye na majalisar Abdul Labaran Madari ya ce jam’iyya mai mulki ta kammala shirinta na rusa Masarautar Bichi tare da maido da tsohon Sarki Sanusi.
Sauran masarautun, in ji shi, za a bar su da kananan hukumomi uku kowacce kamar yadda jaridar Aminiya ta rawaito.