HOTO: Al’umma a Kano sun koka matuka kan masu hakar yashi da ma’adanai

Dawakin Tofa, Chediyar, Ingawa, Mogarawa, al'umma, hakar, yashi, ma'adanai, kano, jihar, maradi
Mazauna yankin Chediyar Ingawa da Mogarawa da ke karamar hukumar Dawakin Tofa a jihar Kano, sun yi kakkausar suka ga mummunan tasirin hakar yashi da ake yi a...

Daga: Uzair Adam

Mazauna yankin Chediyar Ingawa da Mogarawa da ke karamar hukumar Dawakin Tofa a jihar Kano, sun yi kakkausar suka ga mummunan tasirin hakar yashi da ake yi a yankinsu.

Sun fusata cewa hakar yashi ba wai kawai ya tarwatsa harkokinsu na yau da kullun ba, ta hanyar rufe sararin samaniya da kura da lalata duk wani abu da aka ajiye a waje amma yana shafar gonakinsu.

A cewar mazauna yankin, aikin hakar ma’adinan na barazana ga jindadin su, yayin da suke ci gaba da shakar iska mai kura tun lokacin da masu ginin suka fara aikin hakar ma’adinai a yankin.

Karin labari: Da Dumi-Dumi: Majalisar dokokin jihar Kuros Riba ta tsige kakakinta

SolaceBase ta rawaito cewa ana zargin gwamnatin tarayya ce ke gudanar da aikin hakar yashi a cikin al’umma don aikin gina layin dogo na Kano zuwa Maradi.

“Mun Zaɓi Ayyukan Dare” – Jama’a.

Wakilinmu wanda ya ziyarci wurin da ake hakar ma’adinan a karshen mako, ya tattara bayanan cewa, masu aikin hakar yashi suna kwashe sama da tireloli 500 na yashi a kullum.

Daya daga cikin mazauna yankin, Malam Adamu Muhammad ya ce, “Haka yashi a cikin al’ummarmu yana da muni. Kullum muna shakar iska mai ƙura, kuma ba ma iya wanke tufafinmu sai dai idan da dare ne masu tono yashi suka daina aiki” in ji shi.

Karin labari: Gwamnan Kano ya nemi haɗa kai da kasar Netherland kan habaka noma da dakile illolin sauyin yanayi

Wani mazaunin garin Nasir Hassan ya ce, “Mun tashi ne muka iske masu hakar yashi suna fitar da yashi, kuma ba mu ma san daga ina suka fito ba.

Ya ci gaba da cewa, “Mun ga sun share wa manyan motocinsu hanyoyi. Ba mu da farin ciki ko kaɗan. Muna fuskantar ƙalubale da yawa kuma ba za mu iya hana su ba. Muna fatan gwamnati za ta sa baki.”

“Gonakin mu na cikin hadari” – Al’umma.

Malam Muhammad ya kara da cewa gonakinsu na cikin hadari, yana mai cewa, “Ba mu da filayen noma da yawa, kuma a yanzu wannan aikin yana daukar fiye da haka.

Karin labari: Hukumar INEC ta karbi wasika daga mazabu na sake kiran dan majalisar wakilai

Ya kara da cewa, baya ga kalubalen da aka ambata, kananan hanyoyin da suke amfani da su wajen kiwon shanun nasu yanzu ba su da amfani saboda aikin da ake yi.

Wani mazaunin garin Malam Sama’ila Abubakar ya koka da cewa, “Ayyukan da suke yi ya shafi gonakinmu. Mun kai karar hakimin mu da hukumomin da abin ya shafa, amma duk a banza.”

“Da farko sun kwace sunayen mu, inda suka yi alkawarin biyan diyya. Sai dai daga baya sun ce babu bukatar a biya mu diyya domin za mu iya komawa mu kwashe gonakinmu da zarar sun kammala aikinsu.”

Karin labari: Hukumar NEDC ta kara himmatuwa don inganta ilimi a jihar Gombe

“Hakan ce ta sa ba za mu iya yin komai a kai ba, sai dai mu yi addu’ar Allah ya sa mu dace kawai,” Malam Abubakar ya koka sosai.

“Ba za mu iya zuba ido mu bar barna ta same ku ba” –  Gwamnatin Kano ta mayar da martani.

Gwamnatin jihar Kano ta sha alwashin cewa ba za ta nade hannunta tare da barin barna ta afkawa mazauna yankin Chediyar Ingawa da Mogarawa ba.

Kwamishinan kasa da tsare-tsare, Abduljabbar Muhammad Umar ne ya bayyana haka a wani taron manema labarai a karshen mako.

Karin labari: Wasu ‘yan ta’addar ISWAP sun kashe DPO tare da raunata mutum 2 a Borno

Umar ya jaddada cewa gwamnatin jihar Kano ba za ta tsaya tsayin daka ba wajen barin ayyukan hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba su jefa al’umma cikin hadari.

Ya nanata cewa gwamnatin Kano ba za ta amince da ayyukan hakar ma’adinai ba bisa ka’ida ba da ke kawo hadari ga al’umma.

An dai jiyo shi yana cewa, “Saboda haka, an hana duk wani aikin hakar yashi da ma’adinai har sai Gwamna Abba Kabir Yusuf ya amince da shi.”

Dawakin Tofa 2 Dawakin Tofa 3 Dawakin Tofa 4

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here