‘Yan ta’adda sun kai harin hadin gwiwa hedkwatar ‘yan sanda da fadar Sarki a Yashikira dake Karamar Hukumar Baruten ta Jihar Kwara da tsakar dare, inda suka kone wani wani bangare na fadar.
Harin ya jefa mazauna cikin firgici kuma ya girgiza tsarin sarautar gargajiya.
Lamarin ya faru ne da misalin karfe 2:00 na safe ranar Litinin, a cewar rahotanni.
Maharan masu yawa, sun mamaye yanki inda suka kai hari a lokaci guda hedkwatar ‘yan sanda ta Yashikira da fadar Sarkin Yashikira.
Shaidun gani da ido sun ce maharan sun tsaya na tsawon mintuna suna harbi mai karfi a Yashikira dake Karamar Hukumar Baruten ta Jihar Kwara arfi, lamarin da ya sa mazauna suka tsere zuwa cikin daji domin tsira yayin da sautin harbi ke ƙara fita a ko’ina cikin al’umma.
A yayin harin, an sace mutane kusan goma, inda aka kai su wajen da ba a sani ba.
Duk da haka, an ce Sarkin Yashikira ya tsira daga harin lafiya lau, ko da yake an samu dan rudani na dan lokaci a cikin fada yayin mamayar.
Harin ya kara tsananta tsoro a Karamar Hukumar Baruten, wani yanki da ke kan iyaka wadda kungiyoyin masu dauke da makamai ke yawan kai hari saboda wuyar yanayin kasarta da kusancinta da hanyoyin da ke haɗa jihohi.
Hukumomin yankin sun tabbatar da cewa wasu mata da yara na cikin wadanda lamarin ya shafa, kodayake har zuwa wannan lokacin da aka tattara wannan rahoto ba a gama tantance adadinsu ba.
Da yake magana kan lamarin, shugaban Karamar Hukumar Baruten, Issa Jubril, ya ce: “Sarkin ya samu kubuta yayin lamarin.”
Da aka tambaye shi ko an sace wasu mata da yara daga fada, Issa ya ce, “Eh, amma ba zan iya ba ku adadi da sunayen wadanda lamarin ya shafa yanzu ba.
“Amma Sarkin yana cikin koshin lafiya, kuma garin ya dawo daidai yanzu. Nan da nan muka yi kokari sosai don sanar da hukumomin tsaron da suka dacewa, kuma suna kan lamarin,” inji shi.
A cewar mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Jihar Kwara, SP Adetoun Ejire-Adeyemi, Kwamishinan ‘yan sanda, Ojo Adekimi, ya ba da umarnin gudanar da cikakken aiki na kwarewa da ya kunshi ‘yan sanda, sojoji, masu gadin dazuzzuka, da kungiyoyin ‘yan banga don ceto wadanda aka sace da bibiyar maharan.
Rundunar ta kuma tabbatar da cewa an kara jami’an tsaro ga yankunan da ke cikin hadari a jihar.












































