Dole ne jami’o’i su zama hanyoyin bunkasa masana’antu, ba wai wuraren koyo kawai ba — Shettima

Kashim Shettima sabo 750x430

Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima, ya ce dole ne jami’o’in Najeriya su zama cibiyoyin kirkire-kirkire, kasuwanci, da bunkasa masana’antu domin hanzarta bunkasar tattalin arziki da kuma cimma burikan ci gaban kasar.

Shettima ya bayyana hakan ne a ranar Litinin yayin kaddamar da sashen kirkire-kirkire na fasahar kera kayayyakin jami’o’i (Manu-Tech UniPod) a Jami’ar Aikin Gona ta Michael Okpara da ke Umudike, a Karamar Hukumar Ikwuano.

An tsara wannan ne domin bunkasa kirkire-kirkire na fasaha da harkar kasuwanci.

Wannan shiri wani abu ne na musamman da kirkire-kirkiren kayayyaki ta hanyar dijital wadda Hukumar Raya Kasashe ta Majalisar Dinkin Duniya (UNDP) ta kafa, tare da hadin gwiwar Gwamnatin Tarayya ta hannun Asusun Tallafawa Manyan Makarantu na (TETFund).

Mataimakin Shugaban Kasa, wanda Ministan Ilimi, Dr Tunji Alausa ya wakilta, ya ce shirin ya nuna Ajandar Sabunta Fatan (Renewed Hope Agenda) ta Shugaba Bola Tinubu, wadda ke ba da fifiko ga ilimi, kirkire-kirkire, bunkasa masana’antu, tallafa wa matasa da kuma karkata akalar tattalin arziki.

Ya ce Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya tana aiwatar da Tsarin Sabunta Fannin Ilimi a Najeriya domin karfafa ilimin, sana’o’i, dijital, bincike, kirkire-kirkire, kasuwanci da bunkasa masana’antu a fadin kasar.

“Nan gaba Jami’a dole ne ta samar da masu kirkire-kirkire, ‘yan kasuwa, masu kera abubuwa da masu samar da ayyukan yi. Dole ne jami’o’inmu su zama matattarar kafuwar masana’antu,” in ji Shettima.
Gwamnan Jihar Abia, Alex Otti, ya ce hadin gwiwa tsakanin masana kimiyya da na masana’antu ta hanyar shirin zai sake fassara ma’anar kera kayayyaki, kirkire-kirkire da ci gaban tattalin arziki a jihar.

Otti ya ce wannan cibiya za ta karkata binciken jami’o’i wajen magance matsalolin yau da kullum, samar da kayayyakin da za su yi amfani a kasuwa da kuma samar da kudade ga ayyukan kasuwanci a fadin jihar da ma shiyyar baki daya.

Mataimakiyar babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Mrs Ahunna Eziakonwa, ta ce sashen kirkire-kirkiren ya wuce kawai a dube shi a matsayin aikin ci gaba.

Eziakonwa, wadda kuma ita ce Darekta a Ofishin UNDP na Shiyyar Afirka, ta bayyana shirin a matsayin wani bangare na Shirin Timbuktoo na UNDP. Wannan shiri yana da nufin tara dalar Amurka biliyan daya domin tallafa wa sabbin sana’o’i guda 10,000 na Afirka, fadada gudanarwar kasuwanci guda 1,000 da kuma samar da ayyukan yi na gari guda miliyan 10 a fadin nahiyar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here