Hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Jigawa (JISIEC), ta sanya ranar 5 ga watan Oktoba domin gudanar da zaben kananan hukumomi a jihar.
Shugaban hukumar Alhaji Awwal Muhammad ya bayyana haka a taron masu ruwa da tsaki, a Dutse ranar Juma’a.
Muhammad ya tabbatar da shirin hukumar na gudanar da sahihin zabe a kananan hukumomi 27 na jihar.
Ya bayyana cewa a baya hukumar ta sanar da dage zaben kansiloli, daga watan Yunin 2024, zuwa watan Yunin 2025, bayan gyaran dokar zaben jihar.
Karin labari: Gwamnatin tarayya ta musanta rage alawus alawus din dalibai
“Duk da haka, kuna sane da hukuncin Kotun Koli na baya-bayan nan da ta umurci dukkan gwamnatocin jihohi, da su kafa majalisun kananan hukumomin da aka zaba ta hanyar dimokiradiyya a jihohinsu, nan take.
“A bisa bin hukuncin da kotun koli ta yanke na baya-bayan nan, JISIEC, a matsayinta na hukumar shari’a, ta ga ya zama dole ta koma ga hukuncin da ta yanke a baya kan zaben kananan hukumomi, sannan ta bukaci baki daya da a sake gyara dokar zaben jihar, domin ta bi hukuncin kotun koli. , saboda haka ya sanya ranar Asabar 5 ga waan Oktoba, 2024 a matsayin sabuwar ranar da za a gudanar da zaben kananan hukumomi a jihar Jigawa,” inji shi.
Karin labari: Shugaba Tinubu ya daga likafar fanshon jami’an sojin ruwa
Don haka ya bukaci hukumomin tsaro, shugabannin gargajiya da na addini da jam’iyyun siyasa da kungiyoyi harma da kungiyoyin mata da shugabannin matasa da dukkan kafafen yada labarai da kungiyoyin al’umma da su marawa hukumar baya, domin cimma burin da ake so.
Muhammad, wanda ya jaddada kudirin hukumar na gudanar da sahihin zabe, ya yabawa masu ruwa da tsaki bisa goyon bayan da suke baiwa hukumar, a kokarinta na gudanar da zaben kansiloli cikin gaskiya da adalci a jihar a cewar NAN.